logo

HAUSA

WHO ta yi kira da a cike gibin rashin daidaito a fannin kiwon lafiya yayin bazuwar annoba

2021-04-07 12:09:31 CRI

WHO ta yi kira da a cike gibin rashin daidaito a fannin kiwon lafiya yayin bazuwar annoba_fororder_tedros

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi kira da a samar da tsarin inganta kiwon lafiyar al’ummun duniya, yayin da ake tsaka da fuskantar cutar COVID-19, wadda ta kara fito da wagegen gibin dake akwai, a fannin kiwon lafiya da tallafawa al’umma tsakanin kasashe daban daban.

Tedros ya yi wannan kiran ne a jiya Talata, gabanin bikin ranar lafiya ta bana da za a gudanar a yau Laraba, yana mai cewa "Duk da cewa annobar COVID-19 ta shafi kowa da kowa, talakawa da mawadata, amma marasa galihu sun fi dandanar radadin ta, ta fuskar rasa rayuka da bakatun yau da kullum.

Babban daraktan na WHO, ya kuma yi kira da a samar da daidaito a fannin mallakar fasahohin yaki da COVID-19 a ciki da kuma tsakanin kasashe, kana a samar da tsare tsaren gaggauta yin gwaji, da samar da iskar oxygen, da jinya tare da rigakafin cutar.

Ya ce wani muhimmin batu shi ne karfafa shirin COVAX, wanda WHO ke jagoranta da nufin samar da rigakafi ga duniya baki daya, shirin da kawo yanzu ke fuskantar karancin damar raba rigakafin yadda ya kamata, da kuma matsalar gibin kudin aiwatar da shi, da suka kai dalar Amurka biliyan 22.1.

Alkaluman hukumar WHO, sun nuna cewa, wannan annoba ta jefa tsakanin mutane miliyan 119 zuwa miliyan 124 cikin matsanancin talauci a shekarar 2020, yayin da sahihan shaidu suka nuna yadda aka samu karuwar gibi tsakanin jinsi a fannin guraben ayyukan yi, ta yadda mata suka rasa gurabe sama da takwarorin su maza, cikin sama da watani 12 da suka gabata. (Saminu)

Saminu