logo

HAUSA

Kamfanin Huawei na aikin fadada fasahar 4G zuwa wasu biranen Habasha

2021-04-07 10:46:28 CRI

Kamfanin Huawei na aikin fadada fasahar 4G zuwa wasu biranen Habasha_fororder_habasha

Babban kamfanin fasahar sadarwa na kasar Sin Huawei, ya ce yana aikin fadada fasahar 4G zuwa wasu manyan biranen kasar Habasha 6, dake arewa maso yammacin kasar.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ta ce Huawei na aiki tare da kamfanin Ethio-Telecom, don fadada fasahar 4G zuwa sama da birane 12, a yankin na arewa maso yammacin kasar Habasha.

Sanarwar ta kara da cewa, fatan kamfanin Huawei shi ne kaddamar da fasahar 4G a yankin, ta yadda hakan zai baiwa al’ummunsa damar more hidimar sadarwa mai nagarta.

Bayan shafe shekaru sama da 20 kamfanin na aiki a Habasha, yanzu haka Huawei ya samar da guraben ayyukan yi sama da 300, kuma al’ummun kasar sama da miliyan 45 na more hidimomi, da ayyukan da kamfanin ya kammala.

Ko da a watan Fabarairun da ya shude ma, kamfanin Ethio-Telecom ya bayyana cewa, kamfanin ZTE na kasar ya fara aiwatar da fadada hidimar fasahar 4G, don kyautata hanyoyin sadarwa a manyan biranen tsakiyar kasar 6.

Yanzu haka dai Habasha na fadada ayyuka a fannin zamanantar da hidimomin sadarwa, da tallafin kamfanonin kasar Sin, a yunkurin da kasar ta gabashin Afirka ke yi, na shiga a dama da ita wajen cin gajiya, da kuma bunkasa tattalin arziki mai nasaba da fasahar sadarwa, ta hanyar samar da hanyoyin sadarwa masu karfi, da fadi, da kuma sauri. (Saminu)

Saminu