logo

HAUSA

Jami’in MDD: Samar da makamashi mai tsafta zai taimakawa shirin yaki da sauyin yanayi a Afrika

2021-04-07 10:29:01 CRI

Jami’in MDD: Samar da makamashi mai tsafta zai taimakawa shirin yaki da sauyin yanayi a Afrika_fororder_210307-makamashi mai tsabta

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya ce, tallafawa Afrika wajen shirin yaki da sauyin yanayi yana da matukar muhimmanci, inda ya bukaci a kara daukar matakan samar da makamashi mai tsafta ga miliyoyin mutanen da har yanzu ba su da damar samun lantarki mai rangwame.

Guterres ya bayyana a wani taron tattaunawa da shugabanni ta intanet wanda bankin raya ci gaban Afrika ya shirya, ya ce a matsayinta na nahiyar dake da karancin haifar da matsalolin sauyin yanayi, Afrika tana matukar bukatar tallafi da goyon baya mai karfi.

Ko da yake Afrika tana da albarkatu masu tarin yawa na makamashi mai tsafta, amma ta samu kaso 2 cikin 100 ne kacal na yawan jarin da aka zuba a duniya a fannin samar da makamashi mai tsafta a cikin sama da shekaru 10 da suka wuce, kamar yadda ya bayyana.

Tsoffin hanyoyin bunkasa ci gaba da yadda ake amfani da makamashin sun gaza wajen samarwa mutanen Afrika damar bai daya ta amfani da makamashi mai tsafta, a cewar jami’in, hakan na nufin daruruwan miliyoyin mutane har yanzu suna da karancin makamashi da kuma rashin lantarki mai rangwame ko kuma suna amfani da makamashin girki dake gurbata muhalli ko kuma wanda ke haifar da illa.

Babban sakataren MDD ya ce, za a iya samar da tsarin bai daya na damammakin amfani da makamashi a Afrika ta hanyar samar da makamashi mai tsafta. Ya bukaci a samar da wani cikakken tsarin taimakawa nahiyar wajen cimma burin da aka sanya gaba gabanin babban taron kasa da kasa kan sauyin yanayi na COP26, wanda ake sa ran gudanarwa a watan Nuwamba. (Ahmad)