logo

HAUSA

IMF: Tattalin arzikin Sin zai samu karuwa na kashi 8.4% a bana

2021-04-07 13:33:45 CRI

IMF ta gabatar da rahoton hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya a jiya Talata, inda ya yi hasashen cewa, karuwar tattalin arzikin duniya a bana zai kai kaso 6%, wanda zai dara na watan Janairu da kashi 0.5%.

An yi kiyasin cewa, wannan adadi a kasar Sin, zai kai kashi 8.4%, wanda zai karu da kaso 0.3% bisa na hasashen da hukumar ta yi a watan Jarairu. Ban da wannan kuma, rahoton ya yi hasashe cewa, yawan karuwar tattalin arzikin kasashe masu wadata zai kai kaso 5.15%, yayin da na kasashe da kasuwa masu tasowa zai kai 6.7%.

Rahoton na ganin cewa, babu tabbacin makomar karuwar tattalin arzikin duniya baki daya, kuma hakan zai danganta da halin cutar COVID-19, da matakan kandagarki da duniya ke aiwatarwa. (Amina Xu)