logo

HAUSA

Sin na fatan kasar Amurka za ta cika alkawarinta na kare hakkin dan Adam da kawar da ra’ayin nuna wariya ga kananan kabilu

2021-04-06 20:39:09 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, a kasar Amurka, ra’ayin nuna wariya ga launin fata ya dade yana faruwa a dukkan fannoni a kasar. A don haka kasar Sin, na fatan kasar Amurka za ta cika alkawarinta na kare hakkin dan Adam, da yaki da ayyukan nuna wariya ga launin fata kan kananan kabilu ciki har da Amurkawa ‘yan asalin Asiya, da tabbatar da hakkinsu, da kawar da ra’ayin nuna wariya ga launin fata a kasar, da kawar da tsoron da cin zarafin da ake yi musu.

A kwanakin baya, jaridar The New York Times ta gabatar da wani bayani mai taken karuwar rikice-rikice kan ‘yan asalin Asiya, inda aka yi nuni da cewa, tun daga watan Maris na bara zuwa yanzu, yawan lamuran nuna wariyar launin fata a fadin kasar Amurka ya zarce 110. Wani rahoto da jami’ar jihar California ta kasar Amurka ta fitar a baya, ya nuna cewa, yawan laifuffukan da aka aikata kan ‘yan asalin Asiya a kasar Amurka a shekarar 2020 ya karu da kashi 149 cikin dari. (Zainab)