logo

HAUSA

Denja Abdullahi: Fassarar littattafan kasar Sin zuwa harshen Hausa zai taimakawa al’ummar Najeriya kara fahimtar al’adun Sin

2021-04-06 15:09:29 CRI

Denja Abdullahi: Fassarar littattafan kasar Sin zuwa harshen Hausa zai taimakawa al’ummar Najeriya kara fahimtar al’adun Sin_fororder_微信图片_20210402150648

A cikin shirinmu na makon da ya gabata, Murtala Zhang ya zanta da Malam Denja Abdullahi, shugaban asusun kula da harkokin rubuce-rubuce mai suna “Orpheus Literary Foundation” dake Najeriya, kana darektan hukumar fasaha da al’adu ta kasar reshen jihar Bauchi, wanda kuma shi ne tsohon shugaban kungiyar marubutan Najeriya baki daya, ko kuma ANA a takaice.

A zantawar tasu, malam Denja Abdullahi ya bayyana yadda suka hada kai tare da kamfanin fassara da dab’i na kasar Sin, wato “China Translation and Publishing House” a turance, domin kokarin fassara wasu littattafan kasar Sin biyar, daga yaren Turanci zuwa Hausa tun daga shekara ta 2016. Ya kuma bayyana yadda suka gudanar da ayyukan fassara, gami da ma’anar fassara littattafan Sin zuwa harshen Hausa, wanda shi ne daya daga cikin manyan harsuna a yankunan yammacin Afirka.

A cikin shirinmu na wannan mako, za mu sanya muku ragowar hirar Murtala Zhang da malam Denja, inda malam Denja ya bayyana cewa, fassara littattafan kasar Sin daga Turanci zuwa Hausa, ba raya harshen Hausa kawai zai yi ba, har ma zai taimakawa al’ummar Najeriya kara fahimtar kyawawan al’adun gargajiya, gami da halayen al’ummar kasar Sin.

Malam Denja ya kuma bayyana kyakkyawan fatansa ga dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya.(Murtala Zhang)