logo

HAUSA

Sin ta fitar da takardar bayani game da aikin rage talauci

2021-04-06 12:40:34 CRI

Ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da aikin da gwamnati ke yi na rage talauci a kasar. Takardar wadda aka fitar a yau Talata, mai taken "Rage talauci: kwarewar kasar Sin da gudummawarta, ta fayyace bayanai game da hanyar da Sinawa suka bi, wajen cimma muhimmiyar nasarar kawar da matsanancin talauci, da gabatar da salon kasar Sin, tare da raba kwarewarta, da matakai na yaki da fatara.

Baya ga budewa da kuma bangaren rufewa, takardar ta kunshi sauran sassa 5: Ciki har da babi game da muhimmin alkawarin JKS, da babi game da nasarar yaki da matsanancin talauci, da babin dabarun tunkarar kebabbun sassan rage talauci, da na gano sabbin hanyoyin rage talauci, da na aikin dake gaban daukacin bil adama game da samar da al’umma mai makomar bai daya wadda za ta kubuta daga fatara.

Kaza lika takardar ta tabo batun kasancewar bana shekarar da JKS ke cika shekaru 100 da kafuwa, tana mai cewa, jam’iyyar ta hade wuri guda, tare da jagorantar Sinawa, a yakin da suke yi da fatara cikin yakini, da aniyar cimma nasara a duk tsawon wannan karni.

Ta kuma ce Sin ta kasance kasa dake da kaso daya bisa 5 na daukacin yawan al’ummun duniya, kuma matakin ta na yakar matsanancin talauci daga dukkanin fannoni, wata muhimmiyar nasara ce a tarihinta, da ma tarihin bil adama baki daya.    (Saminu)