logo

HAUSA

Kasar Sin tana hadin gwiwa tare da sauran kasashe a fannin samar da allurar rigakacin COVID-19

2021-04-06 12:21:48 CRI

Kasar Sin tana hadin gwiwa tare da sauran kasashe a fannin samar da allurar rigakacin COVID-19_fororder_20210406-Bello-allura

A yayin da duniyarmu ke ci gaba da fama da annobar cutar COVID-19, kasar Sin tana kokarin hadin gwiwa tare da sauran kasashe, ta hanyoyi daban daban, don samar da isassun alluran rigakafin cutar da ake bukata.

A kwanakin baya, alluran rigakafin cutar COVID-19 rukuni na biyu, da kasar Zimbabwe ta saya daga kasar Sin, sun isa birnin Harare. Daga baya, wata mace mai suna Deborah Birch, mai shekaru 65 a duniya, ta karbi allurar rigakafi kirar kasar Sin, bisa shawarar da likitoci suka ba ta. A cewar Madam Birch,

“Bayan karbar allurar rigakafin, hankalina ya kwanta. Ina da imani sosai kan ingancin allurar rigakafin kirar kasar Sin. Domin likita ya gaya mana cewa, ya fi son allurar rigakafin COVID-19 ta kasar Sin, ta la’akari da nau’in allurar, wadda aka tsara ta bisa kwayoyin cutar da aka riga aka kashe su. Ban da wannan kuma, an gudanar da gwaje-gwaje kan allurar, don tabbatar da ingancin ta.”

Allurar rigakafi ita ce makamin da ake iya yin amfani da shi wajen yaki da kwayoyin cutar COVID-19. Don taimakawa kasashe masu tasowa samun wannan makami mai muhimmanci, tun tuni kasar Sin ta yi alkawarin mai da allurar a matsayin wani kaya na jama’ar daukacin duniya. Zuwa karshen watan Maris, kasar Sin ta riga ta ba da tallafin alluran rigakafi ga wasu kasashe 80, da kungiyoyin kasa da kasa guda 3. Kana tana sayar da alluran rigakafi da ta kera ga wasu kasashe fiye da 40. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta halarci shirin samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 da hukumar lafiya ta duniya WHO ta gabatar, inda ta yi alkawarin samar da alluran da yawansu ya kai miliyan 10, don biyan bukatun kasashe masu tasowa.

A sa’i daya, kasar Sin tana kokarin hadin gwiwa tare da sauran kasashe, a fannonin tsarawa da samar da alluran rigakafin cutar COVID-19. Zhang Yuntao, shi ne mataimakin shugaban kamfanin hada hadar magani na CNBG na kasar Sin, ya kuma bayyana a wajen wani taron manema labaru da aka kira a kwanakin baya cewa,

“An yi gwaje-gwaje a matakai 3 na ingancin allurar rigakafin cutar COVID-19 da kamfanin CNBG ya samar a wasu kasashe 125, kana bayan da muka mika ta ga kasuwa, al’ummun wasu kasashe fiye da 190 sun yi amfani da ita.”

Ban da wannan kuma, ana kokarin karfafa hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da sauran kasashe, ta fuskar samar da allurar rigakafin cutar COVID-19. A ranar 28 ga watan Maris da ya gabata, an kaddamar da aikin hada alluran rigakafin cutar COVID-19, bisa hadin kan kasar Sin da kasar hadaddiyar daular Larabawa ta UAE, a Abu Dhabi. Inda Sheikh Abdullah Bin Zayed, ministan harkokin wajen kasar UAE ya bayyana cewa, ta hanyar hadin gwiwa tare da kasar Sin, kasarsa na neman zama wata cibiyar hada alluran rigakafin COVID-19 da ta jigilarsu, don ba da taimako ga sauran kasashe, a kokarinsu na dakile annobar COVID-19. Kana, kasar Sin ta yi alkawarin mika ma kasar Brazil sinadaran da ake bukata don hada alluran rigakafin, inda za a yi jigilar alluran a rukunai 14 zuwa kasar Brazil, kafin nan da karshen watan Yuni mai zuwa.

Zuwa yanzu, gamayyar kasa da kasa sun amince da alluran rigakafin cutar COVID-19 kirar kasar Sin, musamman ma ta la’akari da yadda suke da tsaro, da inganci. Zuwa yanzu, wasu manyan kusoshin kasashe daban daban sun riga sun karbi allurar rigakafin kirar kasar Sin, inda suka nuna amincewarsu da ingancin alluran. Cikinsu, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce,

“Ko da yake ana fama da matsalar karancin alluran rigakafin cutar COVID-19 a duniya, amma duk da haka, kasar Sin ta ba da tallafin alluran ga wasu kasashe da dama, tare da taimakawa wasu kasashen samun alluran rigakafin da kasar Sin ta samar. Hakan ya nuna niyyar kasar Sin, ta hadin gwiwa tare da sauran kasashe, don ganin bayan annobar COVID-19 cikin sauri.” (Bello Wang)

Bello