logo

HAUSA

Shirin COVAX ya samar da sama da alluran rigakafin COVID-19 miliyan 36 ga kasashe 86

2021-04-06 11:06:46 CRI

Kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya ce shirin nan na tabbatar da daidaito wajen raba alluran rigakafin cutar COVID-19 mai lakabin COVAX, wanda ake aiwatarwa karkashin jagorancin hukumar lafiya ta duniya WHO, ya samar da sama da alluran rigakafin COVID-19 miliyan 36 ga kasashe 86.

Stephane Dujarric, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron ganawa da manema labarai, ya ce ya zuwa karshen makon da ya gabata, karkashin shirin na COVAX, kasar Algeria ta karbi sama da rigakafin COVID-19 36,000, matakin da ko shakka ba bu zai taimaka, wajen hanzarta shirin kasar na yiwa al’ummunta rigakafin.

Jami’in ya rawaito babban jami’in tsare tsare na hukumar WHO a Algeria Eric Overvest, na cewa sabbin alluran rigakafin da aka samar, za su baiwa kasar damar yiwa kowa rigakafin. Mr. Overvest ya kara da cewa, jami’an WHO sun shirya tsaf, don ganin sun taimaka wajen horas da jami’an lafiyar kasar, da fadakar da al’umma game da rigakafin, tare da tabbatar da nagartar wuraren ajiya.

A Laos kuwa, babbar jami’ar tsare tsare ta hukumar WHO a kasar Sara Sekkenes Tollefsen, cewa ta yi tuni kasar ta yiwa sama da mutane 4,000 rigakafin na COVID-19 wanda shirin COVAX ya samar, ciki har da jami’an lafiya dake kan gaba wajen yaki da cutar. Sara Sekkenes Tollefsen, ta ce WHO na taimakawa Laos wajen cimma nasarar gangamin rigakafin da aka fara a kasar tun daga ranar Juma’ar makon jiya.  (Saminu)