logo

HAUSA

Kalubalen yaki da ta’addanci a Xinjiang

2021-04-02 10:40:18 CRI

Yankin Xinjiang dake yammacin kasar Sin, ya zama daya daga cikin hanyoyin cinikayya na farko kuma mafi muhimmanci ga duniya, wadda ake kira da Hanyar Siliki, da ta hada tsohuwar kasar Sin da yammacin duniya.

Sai dai yankin bai kasance mai kwanciyar hankali ba. Daga shekarar 1990 zuwa 2016, ya yi fama da dubban hare-haren ta’addancin da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama, da daruruwan jami’an tsaro. Nau’ikan hare-haren da aka kai yankin, sun jefa tsoro da fargaba a zukatan jama’a. Yawan asarar da aka yi a yankin ba zai kimantu ba, yayin da kwanciyar hankali ya yi masa karanci. Sai dai duk da haka, hukumomi sun dage wajen kokarin dawo da zaman lafiya a wannan yanki.

Cikin shirye-shiryen bidiyo na farko guda 3 da gidan talabijin na CGTN ya gabatar dangane da yaki da ta’addanci a Xinjiang, an gabatar da wasu hotunan bidiyo masu tayar da hankali da ba a taba gani ba, wadanda suka auku a Xinjiang, tare da nuna juriya irinta al’ummar yankin.

Shiri na 4 kuma mai taken “"The war in the shadows: Challenges of fighting terrorism in Xinjiang" da za a nuna a yau a sahfin Intanet ya bayyana tunanin masu tsattsauran ra’ayi da kalubalen da kokarin kasar Sin ke fuskanta na dakile ta’addanci a ciki da wajen Xinjiang. (Fa’iza Mustapha)