logo

HAUSA

A idanun ‘yan jaridan kasashen waje: An shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta shekarar 2022

2021-04-02 14:10:15 CRI

A idanun ‘yan jaridan kasashen waje: An shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta shekarar 2022_fororder_6O2A6923

A idanun ‘yan jaridan kasashen waje: An shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta shekarar 2022_fororder_6O2A6930.JPG

A idanun ‘yan jaridan kasashen waje: An shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta shekarar 2022_fororder_6O2A7000.JPG

Koda yake fure na budewa a birnin Beijing, amma a birnin Zhangjiakou dake da nisan kilomita fiye da 200 daga birnin Beijing, wato wuri daya ne da za a gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022, ana samun kankara mai taushi a ko ina a birnin. Wasu ‘yan jaridan kasashen waje sun kai ziyara wajen, inda suka iya ganin masu yawon shakatawa da dama suke jin dadin wasan kankara mai taushi.

A birnin Zhangjiakou, ‘yan jaridan kasashen waje sun kai ziyara a wurare daban daban, kamar kauyen ‘yan wasa masu halartar gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu, da wurin yawon shakatawa na wasan kankara mai taushi na Yunding, da cibiyar wasan gudun kankara mai taushi ta hanyar tsalle daga dandali, da garin wasan kankara na Taizicheng da sauransu, dukkansu sun nuna yabo ga na’urorin wasan kankara da ayyukan shirya gasar da kasar Sin ta yi.

Dan jarida daga kasar Indiya Anil Pandey ya bayyana cewa, Sin ta shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu sosai, kana ta yi aikin kandagarki cutar COVID-19 mai kyau. Gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022 babban batu ne ga kasar Sin, kasar Sin ta gudanar da gasar wasannin Olympics ta shekarar 2008, sake gudanar da gasar wasannin Olympics zai sa kaimi ga daga matsayin kasar Sin a tarihi.

‘Yar jarida daga kasar Romania Ioana Gomoi ta bayyana cewa, tana begen zuwan gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022. Yanzu an gama ayyukan shirya gasar da kashi 80 cikin dari a yankin Zhangjiakou. Ta yi imanin cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022 zai kawo nishadi ga duniya.

‘Yar jarida daga kasar Thailand Tiangroojrat Siwattra ta ce, mutanen kasarta ta Thailand suna son wasannin motsa jiki, ciki har da wasan kankara, a shekarar 2018, ‘yan wasan kasar Thailand sun halarci gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Pyeongchang. Sin da Thailand ba su da nisa da juna, ana samun dakunan wasan kankara na zamani a birnin Zhangjiakou na kasar Sin, tace idan an samu dama, ya kamata mutanen kasar Thailand su zo su yi wasan a wurin.

Dan jarida daga Pakistan Zubair Bashir ya bayyana cewa, yayin da ake yin kokarin tinkarar cutar COVID-19, ana iya shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu, yana da babbar ma’ana sosai. Sin ta farfado da tattalin arzikinta, da samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 ga dukkan duniya, hakan an kawo kyakkyawar makoma ga dukkan duniya. Sin tana son gaya wa dukkan mutanen duniya ta hanyar farfado da wasannin motsa jiki cewa, mu iyali daya ne. Kana ya ce, ya kamata a kawar da yunkurin siyasa da samar da hakikanin gudummawa ga duk dan Adam.

Hoshi Kazuaki wanda ya zo daga kasar Japan wato kasa ce da za ta gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi, ya yi kira ga kasa da kasa da su yi hadin gwiwa don jin dadin gasar wasannin Olympics tare. Ya ce, ana bukatar kasa da kasa da su yi hadin gwiwa a gun gasar wasannin Olympics ta Tokyo, kamar shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, an fi butar a kara yin hadin gwiwa a yayin tinkarar cutar COVID-19. A wannan karo, ya ziyarci birnin Zhangjiakou, ya ga ana gudanar da ayyukan shirya gasar yadda ya kamata, ya yi imani cewa, za a gudanar da gasar cikin nasara idan dukkan duniya za su yi hadin gwiwa da juna.

Manazarci daga kasar Koriya ta Kudu wanda ya taba shiga aikin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Pyeongchang Heejeoung Moon ya gano cewa, karin Sinawa suna son wasan kankara da kuma gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu baki daya. (Zainab)