logo

HAUSA

Hedkwatar majalisar BCI Ta Yi Biris Da Rahotanni 2 Da Ofishin Wakilinta A Shanghai Ya Gabatar Da Ke Tabbatar Da Cewa Babu "Aikin Tilas" A Xinjiang

2021-03-28 17:41:12 cri

Hedkwatar majalisar BCI Ta Yi Biris Da Rahotanni 2 Da Ofishin Wakilinta A Shanghai Ya Gabatar Da Ke Tabbatar Da Cewa Babu "Aikin Tilas" A Xinjiang_fororder_微信图片_20210328174022

Kwanan nan, wasu kamfanonin kasashen waje kamar su H&M da Nike sun yi ikirarin cewa, wai ana samun matsalar "aikin tilas" a jihar Xinjiang, kuma sun bayyana kin amfani da kayayyakin audugar kirar Xinjiang, sanarwar da suka bayar ta jawo hankalin jama'a.

A ‘yan kwanakin da suka wuce kuma, shugabannin wasu kamfanonin auduga a Xinjiang su ma sun nuna cewa, tun shekarar da ta gabata, an soke duk takardun oda na fitar da kayayyakin auduga da aka riga aka sanya hannu ba zato ba tsammani. Me ya sa audugar Xinjiang take fuskantar matsaloli?

A watan Agustan shekarar 2020, Majalisar Ci Gaban Auduga Ta Switzerland (BCI) ta ba da sanarwar soke takardar shaidar tabbaci ga duk kamfanonin auduga na Xinjiang har sai abin da hali yayi. Wannan mataki ya sanya kayayyakin audugar Xinjiang sun shiga cikin jerin sunayen da aka haramta musu cinikin kasa da kasa bisa dalilinta na wai kamfanonin audugar na Xinjiang suna fama da matsalar "aikin tilas". Game da haka, ‘yan kasuwar auduga da ma'aikatan kamfanonin auduga na Xinjiang sun karyata shi.

Me ya sa majalisar BCI ta yanke irin hukunci dake sabanin gaskiya? Wannan na faruwa ne da karyar da wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya suka kirkiro a cikin 'yan shekarun nan.

Tun daga shekarar 2019, wasu kafofin watsa labarai da kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen yamma, ciki har da su Cibiyar Nazarin Manufofin Dabarun Australiya, da kafar watsa labarai ta BBC, da kuma jaridar Wall Street da dai sauransu suna ta yin zargin cewa, wai ana fama da matsalar "aikin tilas" a jihar Xinjiang, har ma suna mayar da masana'antun auduga ta Xinjiang a matsayin "yankin da aka tilastawa aiki sosai".

Domin ba da amsa kan ra'ayoyin jama'a na kasashen waje game da maganar "aikin tilas", ofishin wakilin BCI a Shanghai ya kara gudanar da cikakken bincike kan ayyukansu a Xinjiang kuma a karshe ya tabbatar da cewa, babu wani abu mai kama da "aikin tilas" a jihar. Sun gabatar da rahotanni biyu na binciken ga hedkwatarsa, sannan kuma sun tattara rahotannin binciken na wasu hukumomin bincike kamar SGS ta Switzerland suka bayar a ‘yan shekarun da suka gabata. Amma, hedkwatar BCI ta yi biris da rahotannin tantancewar da ofishin wakilanta na Shanghai da Hukumar SGS suka gabatar, ta ce, akwai matsalar “aikin tilas” a kamfanonin auduga na Xinjiang, kuma babu wani dalili na soke takardar shaidar "Kyakkyawan Auduga" da ta baiwa masana'antun auduga na Xinjiang har abada. A sakamakon haka, audugar Xinjiang kusan tan 500,000 ba za su iya shiga tsarin samar da kayan auduga na kasa da kasa ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)