logo

HAUSA

Kamfanin H&M da Nike ba su da ilmi kan audugar yankin Xinjiang ko kadan

2021-03-25 16:25:57 CRI

Kamfanin H&M da Nike ba su da ilmi kan audugar yankin Xinjiang ko kadan_fororder_微信图片_20210325153252

Kamfanin H&M da Nike ba su da ilmi kan audugar yankin Xinjiang ko kadan_fororder_微信图片_20210325153258

Kwanan baya, kamfanin H&M da Nike da dai sauran kamfanoni, sun nuna adawa ga audugar da yankin Xinjiang ke samarwa, bisa dalilin jita-jitar da aka baza, cewa wai ana tilastawa mutanen yankin Xinjiang yin aiki a wannan sha’ani, abin da ya fusata mutane da dama.

Kowa ya sani, audugar yankin Xinjiang na da inganci matuka, kuma yawan audugar da yankin ke samarwa ba ya biyan dukkanin bukatu a cikin gidan kasar Sin!

Alkaluma na shekarar 2020 da hukumar aikin noma ta yankin ta bayar na nuna cewa, yawan audugar da injuna suka girbe ya kai kashi 69.83%, daga cikinsu a arewacin yankin wannan adadi ya kai 95%. Jita-jitar da aka yi wai kashi 70% aka girbe da hannu ba gaskiya ba ne.

Ko ma dai mene ne, duk wanda ya yi magudi game da gaskiya, tarihi zai yi ramuwar gayya a kan sa. (Amina Xu)