logo

HAUSA

Sin na fatan yin aiki tare da Congo (Brazzaville)

2021-03-25 19:53:18 CRI

Sin na fatan yin aiki tare da Congo (Brazzaville)_fororder_src=http___upload.tjjw.gov.cn_2018_0906_20180906075443952&refer=http___upload.tjjw.gov

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying, ta bayyana cewa, kasarta tana taya al’ummar Congo (Brazzaville) murnar kammala babban zaben kasar cikin lumana, tana kuma taya shugaba Denis Sassou-Nguesso, bisa sake zabarsa da aka yi.  Kasar Sin ta yi imanin cewa, karkashin jagorancin shugaba Sassou, al’ummar Congo (Brazzaville) za su samu sabbin manyan nasarori a fannin bunkasa kasarsu. (Ibrahim Yaya)