logo

HAUSA

Masar ta karbi kashi na biyu na tallafin alluran riga kafin COVID-19 daga kasar Sin

2021-03-23 20:32:48 CRI

Masar ta karbi kashi na biyu na tallafin alluran riga kafin COVID-19 daga kasar Sin_fororder_0323-Masar-Ibrahim-hoto

A yau ne, kasar Masar ta karbi kashi na biyu, na tallafin alluran riga kafin COVID-19 daga kasar Sin. Jakadan kasar Sin dake kasar Masar Liao Liqiang da ministar lafiya ta kasar Masar Hala Zayed, sun shirya wani taron manema labarai a hedkwatar ma’aikatar, inda suka sanya hannu kan takardar shaidar dake tabbatar da mika rigakafin, tare da mataimakin ministan lafiya, harkokin kudi da gudanar da mulki na kasar Masar Wael El Saaey.

Zayed ya shaidawa taron manema labarai cewa, kasar Sin ta baiwa Masar babban taimako da goyon baya, ta hanyar hadin gwiwar gwamnati da kamfanonin kasar ta Sin, abin da ke nuna abotan dake tsakanin shugabannin kasashen biyu, da ma karfin alakar dake tsakanin Masar da kasar Sin. (Ibrahim Yaya)