logo

HAUSA

Wang Yi Ya Bayyana Matsayin Kasar Sin A Bayanin Fara Tattaunawar Manyan Jami’an Sin da Amurka Bisa Manyan Tsare-tsare

2021-03-19 15:02:08 CRI

Wang Yi Ya Bayyana Matsayin Kasar Sin A Bayanin Fara Tattaunawar Manyan Jami’an Sin da Amurka Bisa Manyan Tsare-tsare_fororder_sin

A jiya ne Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya ta Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kana darektan ofishin harkokin waje na kwamitin tsakiyar JKS, da Wang Yi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar sun halarci taron tattaunawar manyan jami’an Sin da Amurka bisa manyan tsare-tsare tare da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da Jake Sullivan, mai ba da shawara ga shugaban Amurka dangane da harkokin tsaro.

Bayan da bangaren Amurka ya bayyana bayanin fara tattaunawar, Wang Yi ya ce, a shekaru da dama da suka wuce, Amurka ta kawo illa ga muhimman muradun kasar Sin ba tare da wani dalili ba, Sin da Amurka sun gamu da babbar matsala wajen raya huldar da ke tsakaninsu. Lamarin da ya kawo illa ga moriyar jama’ar kasashen 2, da kwanciyar hankali da bunkasuwa a duniya. Bai kamata a ci gaba da haka ba. A baya, da yanzu da kuma nan gaba, kasar Sin ba za ta amince da yadda Amurka ta ke sukanta ba. Haka kuma kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. Lokaci ya yi da Amurka za ta daina irin wannan dabi’a.

Wang Yi ya nuna cewa, dazu Amurka ta yi shelar cewa, wasu kasashe na ganin cewa, kasar Sin tana matsa musu lamba. Ko wadannan kasashe sun fada wa Amurkan haka? Ko kuma Amurka ce ta yi tsammani sun fadi hakan? Kowa ya san wace ce kasar da take matsa wa wasu lamba. Tarihi zai nuna hakikanin abubuwa.

Wang Yi ya jaddada cewa, shawarwarin da shugabannin kasashen 2 suka yi a jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin yana da matukar muhimmanci. Ra’ayi daya da suka cimma ya share hanyar dawo da huldar da ke tsakanin kasashen 2 hanyar da ta kamata. Kasashen duniya sun zura ido kan tattaunawar da kasashen 2 suke gudanarwa a Anchorage, sun sa muhimmanci kan ko Sin da Amurka za su nuna sahihanci ko a’a, ko za su samu ci gaba a tattaunawar ko a’a. idan Amurka tana so, kasar Sin za ta hada kai da ita wajen yin musayar ra’ayoyi bisa ka’idar girmama juna, kana kasashen 2 za su sauke nauyi dake bisa wuyansu, za kuma su tafiyar da harkoki yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan