logo

HAUSA

An yiwa shugaban kasar Saliyo da kusoshin gwamnati rigakafin COVID-19

2021-03-16 10:21:49 cri

Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio, ya kasance mutum na farko da aka yiwa allurar riga-kafin cutar COVID-19 a kasar wanda hakan ke nuna an kaddamar da aikin riga-kafin a kasar a hukumance a jiya Litinin.

Mataimakin shugaban kasar Mohamed Juldeh Jalloh da sauran manyan jami’an gwamnatin kasar sun bi sahun shugaban kasar wajen amsar riga-kafin a lokacin bikin kaddamarwar, kana an yiwa ma’aikatan lafiya da dama dake bakin aikin riga-kafin.

Shugaba Bio ya ce, ba zai taba umartar mutanen kasar su karbi riga-kafin ba tare da shi ya fara karba ba. Don haka a matsayinsa na shugaba, dole ne ya zama abin misali, ya kara da cewa, yana godewa dukkan abokan huldar da suka taimakawa kasar, musamman kasar Sin, wajen baiwa Saliyo gudunmawar riga-kafin.

Ministan lafiyar kasar, Austin Demby, ya ce dukkan riga-kafin wadanda suka fito daga kasar Sin da kuma na COVAX an amince za a yi amfani da su a kasar karkashin shirin da hukumar kula da ayyukan gaggawa ta kasar Saliyo ta amince da shi.

Ya ce suna da kwarin gwiwa mai karfi game da riga-kafin, ya kara da cewa, kasar za ta sanya ido sosai a lokacin aikin bayar da riga-kafin domin tabbatar da kiyaye lafiyar dukkan jama’ar kasar.(Ahmad)