logo

HAUSA

Thomas Bach: Sin za ta samar da rigakafi ga ‘yan wasa masu halartar wasannin Olympics

2021-03-12 10:43:46 CRI

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa Tomas Bach, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kwamitin Olympics na kasar Sin zai samar da alluran rigakafin cutar COVID-19, ga ‘yan wasa masu halartar wasannin Olympics da za a gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan a bana, da wasannin Olympics na lokacin hunturu da za su gudana a birnin Beijing na kasar Sin a shekarar 2022 mai zuwa, kana kwamitin na Olympics zai biya kudin sayen alluran.

Mista Bach ya bayyana hakan ne, a cikakken zama na 137 na kwamitin Olympics na kasa da kasa, da ya gudana a jiya, inda ya nuna godiyarsa ga kwamitin Olympics na kasar Sin.

A cewar Mista Bach, kwamitin Olympics na kasar, zai samar da wadannan allurai ne ga mutanen da suke da bukata ta hanyoyi 2: a farko bisa hadin gwiwa da wasu abokan hulda na kasa da kasa, yayin da na biyu zai kasance ta mika wa kasashe da yankuna da suka kulla huldar hadin gwiwa a fannin rigakafin cutar COVID-19 tare da kasar Sin rigakafin kai tsaye.

Bach ya kara da cewa, kwamitin Olympics na kasa da kasa, yana goyon bayan manufar da ake aiwatarwa, ta rarraba alluran rigakafi tsakanin kasashe da yankuna daban daban, bisa wani tsari mai kima. Kana kwamitin ya riga ya sanya hannu kan sanarwar raba rigakafi cikin adalci, wanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta gabatar. (Bello Wang)

Bello