logo

HAUSA

Li Keqing: Sin za ta ci gaba da kyautata muhallin kasar

2021-03-05 11:28:12 CRI

Cikin rahoton aikin gwamnatin da ya gabatar a yau Jumma’a, Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta karfafa aikin rigakafin gurbatar muhalli da kuma inganta aikin kare muhalli, domin ci gaba da kyautata muhallin kasar.

Bisa rahoton da ya gabatar, cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta aiwatar da burin kasa na tunkarar sauyin yanayi nan da shekarar 2030. Sin na da burin rage makamashin da take amfani da shi domin tabbatar da karuwar ma’aunin tattalin arzikin GDP da 13.5%, yayin da za ta rage adadin iska mai gurbata muhalli ta Carbon Dioxide da 18%, kana za a tabbatar da fadin daji da 24.1% a duk fadin kasar. (Maryam)