logo

HAUSA

Kamfanin CanSinoBIO na Sin ya gabatar da bukatar shigar da allurar rigakafinsa na COVID-19 kasuwar hada-hadar kudi

2021-02-26 19:21:50 CRI

A ranar 24 ga wata, jaridar The Wall Street Journal ta Amurka ta wallafa wani rahoto cewa, a wannan rana kamfanin CanSinoBIO na kasar Sin ya sanar da cewa, allurar rigakafinsa yana samar da kariyar da ta kai kaso 65 bisa dari ga alamomin annobar COVID-19, kuma alkaluman da aka fitar bayan mataki na uku na gwajin da aka yiwa mutane a kasashen Pakistan da Mexico da Rasha da Chile da Agentina sun nuna cewa, idan an yi wa mutane allurar rigakafin kamfanin CanSinoBIO sau daya, za su samu kariya kaso 65.28 bisa dari bayan kwanaki 28 daga alamomin cutar, a don haka kamfanin ya bayyana cewa, ya gabatar da bukatar shiga kasuwar cinikin hada-hadar kudi tare da gindaya sharadi, ga hukumar sa ido kan magunguna ta kasar Sin, kuma hukumar ta riga ta karbi bukatarsa.(Jamila)