logo

HAUSA

An hallaka mutane 2 tare da cafke mutum 468 sakamakon tarzomar bayan zabe a jamhuriyar Nijar

2021-02-26 10:45:05 CRI

Ministan ma’aikatar cikin gida da tsaron jamhuriyar Nijar Alkache Alhada, ya ce mutane biyu sun rasa ransu ciki har da wani jami’in tsaro, an kuma cafke mutum 468, biyowa bayan tarzomar da ta barke, bayan ayyana dan takarar jam’iyyar NPDS Mohamed Bazoum, a matsayin wanda ya lashe zagaye na biyu na babban zaben kasar da ya gudana a Lahadin karshen makon jiya.

Mohamed Bazoum dai ya lashe zagaye na biyu na zaben ne da kaso 55.75 bisa dari na jimillar kuri’un da aka kada, yayin da abokin takarar sa Mahamane Ousmane, ya samu kaso 44.25 bisa dari na kuri’un.

Jim kadan da bayyana sakamakon ne kuma, magoya bayan Mahamane Ousmane, suka fara kona tayoyi, da kafa shingaye, tare da yin fito na fito da jami’an tsaro a biranen Yamai, da Zinder da Dosso, a wani mataki na nuna adawa da sakamakon da aka bayyana.  (Saminu)