logo

HAUSA

Jami’ar Johns Hopkins: Yawan mutanen da COVID-19 ta kashe a duniya ya zarce miliyan 2.5

2021-02-26 10:52:35 CRI

Cibiyar bunkasa kimiyya da fasaha ta jami’ar Johns Hopkins CSSE, ta ce, ya zuwa ranar Alhamis yawan mutanen da annobar COVID-19 ta kashe a duniya ya zarce miliyan 2 da dubu 500.

Alkaluman cibiyar ta CSSE sun nuna cewa, adadin mutanen da cutar ta kashe ya kai 2,501,626, yayin da yawan mutanen da suka kamu da cutar a fadin duniya ya zarce miliyan 112.7 ya zuwa karfe 12:24 agogin kasar Amurka daidai da karfe 17:24 na yammaci agogon GMT na wannan rana.

Har yanzu kasar Amurka ce annobar ta fi yiwa barna a duniya, inda yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai 28,348,259 kana cutar ta kashe mutane 506,500, wanda adadin ya zarce kashi 25 bisa 100 na yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya sannan sama da kashi 20 bisa 100 na yawan mutuwar da aka samu a duniya a sanadiyyar cutar.(Ahmad)