logo

HAUSA

Sakamakon kidaya ya tabbatar da Sin ta cimma nasarar fatattakar talauci baki daya

2021-02-26 10:05:28 CRI

Sakamakon kidaya ya tabbatar da Sin ta cimma nasarar fatattakar talauci baki daya_fororder_0226-census-Faeza-hoto

Sakamakon kidayar yaki da talauci ta kasar Sin da aka fitar jiya Alhamis, ya tabbatar da nasarar da kasar ta samu wajen fatattakar talauci.

Wasu majiyoyi daga ofishin yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar, sun ce bisa mizanin da ake da shi yanzu, dukkan mazauna yankunan karkara masu fama da fatara sun yi adabo da talauci.

Majiyoyin sun kara da cewa, kidayar ta samar da sahihan bayanan kididdiga. Wadda ke nuna cewa nasara da kasar Sin ta samu wajen fatattakar talauci na da kwari kuma za ta shafe dogon zango.

A cewar ofishin, an dauki matakai da dama na tabbatar da ingancin kidayar, ciki har da tsarukan kidaya bisa kimiyya da amfani da hanyoyin tattara bayanai ta na’ura.

Daga shekarar 2020 zuwa 2021, sama da ma’aikatan kidaya 210,000 ne suka yi nazari a larduna da yankunan masu cin gashin kai da manyan birane gaba daya guda 22, a sassan tsakiya da yammacin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)