logo

HAUSA

A Najeria an yi jana’izar sojojin kasar 7 da suka mutu a hadarin jirgin sama

2021-02-26 10:32:55 CRI

A jiya Alhamis an binne gawawwakin jami’an sojojin Najeriya 7 da suka mutu a sanadiyyar hadarin jirgin saman yaki da ya faru a makon jiya a kusa da filin jirgin saman babban birnin kasar.

An shiga yanayin dimuwa, yayin da iyalai da manyan jami’an sojojin kasar suka yi bankwana ta karshe da gawawwakin jami’an sojojin da suka mutu a lokacin da suke baki aikinsu sanadiyyar hadarin jirgin saman yaki mai aikin tattara bayanan sirrin a Lahadin da ta gabata.

Jami’an sojojin sun bayar da babbar gudunmawa ga aikin tsaron kasar.

Oladayo Amao, babban jami’in sojojin saman Najeriya ya ce, ko shakka babu a wannan lokaci rundunar sojojin saman kasar tana cikin juyayi da damuwa saboda rashin gwarazan jarumai masu himma da kwazo.

A cewar Amao, hadarin jirgin na ranar Lahadi, yana da alaka da kokarin da dakarun kasar ke yi domin kubutar da ma’aikata da daliban sakandaren kimiyya ta Kagara da aka yi garkuwa da su, a jihar Naija dake shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan jami’an sojojin saman.(Ahmad)