logo

HAUSA

Gwamnonin Najeriya sun lashi takwabin magance matsalar tsaro a yankin arewacin kasar

2021-02-26 20:40:13 CRI

Shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya, kana gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya bayyana kudirin gwamnonin na yin aiki tare da gwamnatin tarayyar kasar, don magance duk wata matsalar tsaro dake damun yankin arewacin kasar.

Gwamnan Lalong ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron gaggawa da kungiyar gwamnonin ta gudanar a jiya, don tattauna kalubalen tsaron dake addabar yankin.

A cewarsa, gwamnonin yankin na arewa, sun kuma nanata kudirinsu na hada kai da takwarorinsu dake sauran shiyyar kasar, don bunkasa hadin kai da zaman lafiya tsakanin dukkan kabilun kasar.(Ibrahim)