logo

HAUSA

Jakadan Najeriya dake Sin: huldar diflomasiyya tamkar aure ce

2021-02-26 18:07:30 CRI

Jakadan Najeriya dake Sin: huldar diflomasiyya tamkar aure ce_fororder_1

Kwanan baya, wakiliyar sashen Hausa ta babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin(CMG) Kande Gao ta yiwa jakadan kasar Nijeriya dake kasar Sin Baba Ahmad Jidda intabiyu, inda jakadan ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, an cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasar Najeriya da kasar Sin. Cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu ci gaba matuka, har an cimma manyan sakamako masu gamsuwa karkashin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Kuma ta fara ne da tambayar jakadan ko wadanne irin nasarori ne aka cimma a cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata karkashin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Najeriyar?