logo

HAUSA

Sin: Sin ta gayyaci jakadun kasashen Turai su ziyarci Xinjiang, amma sun jingirtar ziyararsu

2021-02-26 20:14:12 CRI

Yau yayin taron ganawa da manema labarai, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya gaskanta cewa, sau tarin kasar Sin ta gayyaci jakadun kasashen Turai dake kasar Sin domin su ziyarci yankin Xinjiang, amma abun bakin ciki shi ne, jakadun kasashen na Turai sun jingirtar ziyarar tasu, inda suka gabatar da wasu bukatun da ba su dace ba.

Wang ya bayyana cewa, kasar Sin tana maraba da baki na bangarori daban daban na ketare da su ziyarci yankin Xinjiang, amma wasu kasashen Turai sun gabatar da bukatun da ba su dace ba, alal misali, sun bukaci kasar Sin da ta samar da damar ganawa da fursunonin da suka aikata laifin kawo baraka ga dinkuwar kasar Sin, wannan na nuna cewa, bukatunsu sun saba dokokin kasar Sin, kuma hakan tsoma baki ne a cikin harkokin shari’a na kasar Sin.(Jamila)