logo

HAUSA

An hallaka a kalla mutane 11 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a arewacin Burkina Faso

2021-02-26 10:09:44 CRI

Rundunar sojojin Burkina Faso, ta ce ta hallaka mutane a kalla 11, tare da cafke mutum guda, yayin sumame da ta kaddamar a wasu sassa na kasar, a wani mataki na kakkabe gyauron ‘yan ta’adda, da kuma gano wadanda suka hallaka fararen hula a baya bayan nan.

Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce sojojin kasar sun kaddamar da hare hare a ranekun Talata da Laraba, a lardin Oudalan na yankin arewa maso gabashin kasar. Yankunan da aka aiwatar da matakan sojin sun hada da Tasmakat, da Bidy, da Fourkoussou da kuma dajin Bangao.

Baya ga bata garin da sojojin suka hallaka, sanarwar ta kuma ce, an yi nasarar kwato kayayyakin fada da suke amfani da su.  (Saminu)