logo

HAUSA

Kwararru na kallon nasarar kasar Sin a fannin yaki da talauci a matsayin abu mai karfafa gwiwa

2021-02-26 09:34:04 CRI

Kwararru da masana a fannin samar da ci gaba, na kallon nasarar da kasar Sin ta cimma a fannin yaki da talauci, a matsayin wani mataki dake nuyi ga kwazo, da karfin hali na jagorancin JKS, kuma nasarorin da ake gani a zahiri, za su zamewa sauran kasashe masu tasowa abun koyi.

Da yake tsokaci ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua don gane da hakan a kwanan nan, daraktan cibiyar binciken harkokin da suka shafi kasar Sin a jami’ar Laos Mr. Sithixay Xayavong, ya ce abun da ya fi burge shi, shi ne yadda JKS da al’ummar Sinawa suka yi namijin kokari tare, don cimma wannan nasara, kuma ko shakka babu, nasarorin da Sin ta samu a fannin raya ababen more rayuwa a yankunan karkara, da inganta dabarun noma, sun zamo abun misali ga kasar Laos.

Ita kuwa marubuciya yar kasar Faransa Sonia Bressler, cewa ta yi, kamata ya yi duniya ta yi koyi da irin dabarun Sin na inganta ilimi a yankunan da ake fama da talauci, da samar da tsarin tallafawa al’umma, da wanzar da dabarun hade tsare tsaren ci gaba.

Sonia Bressler ta kara da cewa, al’ummun duniya za su iya cin gajiya daga kwaikwayon manufofin ci gaban Sin na shekaru biyar biyar, wadanda ke kunshe da hadaddun shirye shirye, dake baiwa gwamnati jagoranci wajen ciyar da daukacin al’ummun kasa gaba.  (Saminu)