logo

HAUSA

Sin ta baiwa Saliyo gudunmawar riga-kafin COVID-19 guda 200,000

2021-02-26 10:03:34 CRI

A jiya Alhamis kasar Saliyo ta amshi gudunmawar alluran riga-kafin COVID-19 guda 200,000 daga kamfanin Sinopharm na kasar Sin wanda gwamnatin Sin ta baiwa kasar a matsayin tallafi na shirin aikin riga-kafi ga Saliyo.

Hukumomin lafiyar kasar Saliyo sun bayyana cewa, riga-kafin zai taka muhimmiyar rawa wajen kandagarki da kuma dakile yaduwar cutar ta COVID-19 a kasar.

A cewar hukumomin lafiyar, riga-kafin ya zo a daidai lokacin da gwamnatin kasar Saliyo take shirin yiwa mutane miliyan 1.6 mafiya hadarin kamuwa da cutar riga-kafi a kasar.

Mataimakin ministan harkokin wajen Saliyo, Solomon Jamiru, ya bayyana godiya ga kasar Sin a madadin gwamnatin kasar sakamakon irin tallafin da Sin take baiwa kasar ta Saliyo wajen yaki da annobar, kana ya bada tabbacin zasu cigaba da yin aiki tare da tawagar jami’an kiwon lafiyar kasar Sin domin kawar da annobar COVID-19 a kasar.(Ahmad)