logo

HAUSA

Kalaman Xi Jinping: Me ya sa mutane suke goyon bayan JKS

2021-02-26 20:32:27 CRI

Wani sakamakon nazari da jami’ar Harvard ta wallafa a karshen watan Yuli, ya nuna cewa, sama da kaso 93 na al’ummar Sinawa na nuna goyon baya da ma gamsuwa da JKS.

Tun lokacin da aka kafa JKS a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1921, burin jam’iyyar shi ne faranta ran al’ummar Sinawa da farfado da mafarkin kasar Sin. Kuma wannan shi ya kai jam’iyyar ga samun gagarumar nasarar.

A jawabinsa yayin bikin cika shekaru 95 da kafuwar JKS, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ruwaito wani karin magana dake cewa, “Sai shugaba ya samu goyon bayan wadanda yake mulka, idan ba haka ba zai yi nasara ba”.

Xi ya kan tabo karin magana, ba kawai don ya nuna kwarewa da dasussa da ya koya a tarihi, da ma kira a tuna tsoffin matakan siyasa na mayar da jama’a a gaban komai, amma kuma ya kan jaddada cewa, jam’iyya tana tare da jama’a. Xi, a lokuta da dama, ya sha jaddada cewa, duk abin da jam’iyya ta ke yi, ta kan yi don inganta rayuwar Sinawa, da farfado da burin kasar Sin da tabbatar da zaman lafiya da ci gaban bil-Adama. Haka kuma babu abin da zai hana JKS cimma wannan buri.

Misali shi ne, yadda kasar Sin ta yi nasarar kawar da talauci, abin da ke zama wani abin al’ajabi.(Yaya)