logo

HAUSA

Wane misalin Sin ya kawo wa aikin rage talauci a duniya?

2021-02-26 21:07:05 CRI

Wane misalin Sin ya kawo wa aikin rage talauci a duniya?_fororder_11

Jiya Alhamis 25 ga wata, kasar Sin ta sanar da cewa, ta samu cikakkiyar nasarar kawar da talauci a fadin kasar, wato ta cimma burin da aka tsara a cikin muradun samun dauwamammen ci gaba na MDD nan da shekarar 2030 kafin shekaru goma, musamman ma a cikin shekaru takwas da suka gabata, al’ummun Sinawa kusan miliyan 100 sun fita daga kangin talauci.

Adadin al’ummun kasar Sin ya kai kaso 20 bisa dari na daukacin al’ummun kasashen duniya, a don haka ana iya cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu ba sakamako ne na kasar Sin kawai ba, sakamako ne na duniya.

Wane misalin Sin ya kawo wa aikin rage talauci a duniya?_fororder_22

A matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin yi nasarar kawar da talauci daga duk fannoni, lamarin da ya kara karfafa wa sauran kasashe gwiwa a fannin kawar da talauci, shugaban hukumar yankin Asiya da tekun Pasifik ta asusun raya aikin gona na duniya Nigel Brett ya bayyana cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu ya shaida cewa, kawar da talauci ba mafarki ba ne, ana iya cimma burin idan aka yi kokari.

Abu mafi muhimmanci shi ne, misalin da kasar Sin ta bai wa sauran kasashen duniya ya samar da fasahohi masu ma’ana ga duk duniya.

A sa’i daya kuma, matakan da kasar Sin ta dauka sun taimakawa ajandar samun dauwamammenn ci gaba nan da shekarar 2030 na MDD, a don haka ya dace sauran kasashen duniya su yi nazari kan fasahohin kasar Sin a bangaren , ta yadda za mu gina duniyarmu, da babu talauci tare.(Jamila)