logo

HAUSA

Yadda Sin ta yi abin al’ajabi a yaki da talauci

2021-02-25 21:00:44 CRI

Yadda Sin ta yi abin al’ajabi a yaki da talauci_fororder_1

Yau shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar a nan birnin Beijing cewa, kasarsa ta yi cikakkiyar nasarar kawar da talauci daga duk fannoni, kasar ta Sin ta sake jin wani abin al’ajabi a tarihin bil Adama.

Duba da cewa, a fadin duniya, babu wata kasa wadda ke iya cimma burin fitar da al’ummun kasa sama da miliyan 100 daga kangin talauci a cikin gajeren lokaci kamar haka, musamman ma a cikin shekaru takwas da suka gabata, amma kasar Sin ta fitar muane miliyan 10 daga kangin talauci a cikin kasar a ko wace shekara, saurin da ya burge al’ummun kasashen duniya matuka.

Yadda Sin ta yi abin al’ajabi a yaki da talauci_fororder_2

A cikin rahoton da ya gabatar yayin babban taron da aka kira yau, shugaba Xi ya waiwayi tarihin yaki da talauci na kasar, inda ya tattara fasahohin da kasar Sin ta samu daga fannoni bakwai, dake kumshe da nacewa kan jagorancin JKS, da nacewa kan tunanin mayar da moriyar al’ummun kasa da farko, da nacewa kan tsarin gurguzu da sauransu.

Hakika a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, sakamakon da kasar Sin ta samu wajen yaki da talauci, ya nuna sakamakon da ta samu wajen kare hakkin bil Adama, matakin da zai ciyar da aikin yaki da talauci a duniya gaba yadda ya kamata. Wakilin asusun raya aikin gona na duniya na MDD dake kasar Sin Matteo Marchisio shi ma ya bayyana cewa, kasar Sin ta shaida cewa, yaki da talauci ba mafarki ba ne, ana iya cimma burin a zamanin da muke ciki, kuma wannan muhimmiyar rawar ce da kasar Sin ta taka a aikin rage talauci a duniya.(Jamila)