logo

HAUSA

Tallafin allurar rigakafin COVID-19 da Sin ta baiwa Mozambique sun isa kasar

2021-02-25 12:06:53 CRI

Da yammacin jiya Laraba ne tallafin allurar rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm da kasar Sin ta baiwa kasar Mozambique, suka isa birnin Maputo fadar mulkin kasar.

Shugaban kasar Mozambique Filipe Jacinto Nyusi, ya godewa kasar Sin, kuma firaministan kasar Carlos do Rosario, da wasu jami’an kasar, da kuma jakadan kasar Sin dake kasar Mozambique Wang Hejun, sun karbi rigakafin a filin saukar jiragen saman kasar tare.

Cikin jawabinsa, firaministan kasar Mozambique Carlos do Rosario ya bayyana cewa, zuwan allurar rigakafin cutar COVID-19 ta kasar Sin yana da muhimmiyar ma’ana, wanda zai shiga tarihin kasarsa. A madadin gwamnati, da dukkanin al’ummomin kasar Mozambique, ya nuna godiya ga gwamnati da al’ummomin kasar Sin.

A nasa bangare kuma, jakadan kasar Sin Wang Hejun ya ce, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin ta mai da hankali matuka kan bukatun kasar Mozambique a fannin allurar rigakafin cutar, shi ya sa, ta dauki matakai cikin gaggawa domin samar wa kasar allura, inda kasar ta kasance kan gaba, a jerin wadanda suka samu taimakon allurar rigakafin cutar COVID-19 daga kasar Sin a nahiyar Afirka. (Maryam)