logo

HAUSA

WHO: COVID-19 ta ragu cikin makwanni 6 a jere sai dai sabbin nau’o’in ta na saurin yaduwa a duniya

2021-02-25 10:26:19 CRI

Alkaluman hukumar lafiya ta duniya WHO sun nuna cewa, adadin masu harbuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a dukkanin sassan duniya, sun yi matukar raguwa cikin makwanni 6 a jere, sai dai kuma sabbin nau’o’in cutar na saurin bazuwa.

WHO ta fitar da alkaluman ne cikin rahoton ta na mako mako, inda a jiya Laraba, hukumar ta ce adadin sabbin masu harbuwa da COVID-19 ya ragu da kaso 11 bisa dari tun daga makon da ya gabata, a sassa daban daban ciki har da arewaci da kudancin Amurka, da Turai da Afirka da yammacin Fasifik.

Sassan yankunan arewaci da kudancin Amurka ne ke kan gaba a adadin raguwar masu harbuwa da cutar, inda aka samu raguwar kaso 19 bisa dari, yayin da kasar Amurka ke ci gaba da zama kan gaba a adadin masu harbuwa da cutar, wadanda yawansu a duk mako kan kai mutum 480,467.

A daya bangaren, adadin masu mutuwa sakamakon harbuwa da cutar shi ma ya ragu, inda WHO ta ce raguwar ta kai kaso 20 bisa dari a duk duniya cikin makon da ya gabata.

A cewar wani rahoto na WHO, tun bayan barkewar wannan annoba a duniya, adadin wadanda suka harbu ya kai mutum miliyan 110, kana ta hallaka mutane miliyan 2.5. Kaza lika akwai hasashen karuwar wannan adadi, yayin da ake samun sabbin nau’o’in cutar mafi saurin yaduwa tsakanin al’umma a sassan duniya daban daban. (Saminu)