logo

HAUSA

Kafar watsa labaran Amurka: Yadda JKS ta samu amincewar al’umma

2021-02-25 20:07:46 CRI

Kafar watsa labaran Amurka: Yadda JKS ta samu amincewar al’umma_fororder_1

A gabannin cika shekaru 100 da kafa jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shafin yanar gizo na jaridar The Christian Science Monitor ta Amurka, ya wallafa wani dogon rahoto, inda aka yi nazari kan dalilin da ya sa jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin mai yawan ‘yan jam’iyyar fiye da miliyan 90, wadda ke rike da mulki a babbar kasar Sin mai yawan al’umma sama da biliyan 1 da miliyan 400.

Taken rahoton shi ne “JKS mai dogon tarihin shekaru 100 tana samun karbuwa matuka a cikin kasar Sin, amma wasu kasashen ketare suna zarginta”.

Rahoton ya bayyana cewa, a farkon shekarar 2020, tun bayan barkewar annobar COVID-19, JKS ta gamu da mummunan matsala, rukunonin masu adawa da kasar Sin dake ketare sun zarge ta kamar yadda suke so, amma matakai masu karfi da gwamnatin kasar Sin ta dauka, sun kara karfafa wa al’ummun Sinawa gwiwa, tare da kara nuna wa jam’iyyar goyon baya.

A shekarar 2020 da ta gabata, kasar Sin ta kasance kasa daya kacal wadda ta samu ci gaban tattalin arziki a duniya, kana kasar Sin ta cimma burinta na yaki da talauci cikin nasara karkashin jagorancin JKS, duk wadannan sun sa al’ummun kasar Sin sun kara goyon bayan jam’iyyar.(Jamila)