logo

HAUSA

Wasu kasashen duniya na boye gaskiya da nufin yada karairayi game da Sin in ji jakada Chen Xu

2021-02-25 13:59:14 CRI

Shugaban tawagar Sin dake ofishin MDD na birnin Geneva Chen Xu, ya ce abun takaici ne, ganin yadda wasu kasashen duniya ke kaucewa gaskiya, suna kirkirar karairayi musamman game da jihar Xinjiang, da Tibet da Hong Kong, domin kawai su bata sunan kasar Sin a idon duniya.

Chen Xu wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, a wani bangare na zama na 46, da aka gudanar domin tattauna batutuwa da suka shafi kare hakkin bil adama, ya ce matakan da kasashen ke dauka na nuna karara cewa, burin su shi ne mayar da batun kare hakkin bil adama makami na siyasa.

Yayin zaman dai na Laraba, kasashen Birtaniya da tarayyar Turai, da Jamus, da Amurka, da Canada, da wasu karin kasashen kalilan, sun zargi kasar Sin ba tare da gabatar da sahihan dalilai na gaskiya ba.

Da yake mai da martani game da hakan, Chen ya ce idan har da gaske ne wadannan kasashe, na da burin yayatawa, ko kare hakkokin bil adama, da ba su rura wutar yake yake a sassan duniya daban daban ba, irin yake yaken da suka haifar da rasa rayukan dimbin fararen hula, tare da raba karin wasu da dama da matsugunnan su.    (Saminu)

Saminu