logo

HAUSA

Kasar Sin za ta yayata raba alluran riga kafin COVID-19 a duniya bisa daidaito

2021-02-25 20:38:54 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya sanar a yau Alhamis din nan cewa, gomman kasashe sun amince da yin amfani da alluran riga kafin da kasar Sin ta samar na gaggawa, haka kuma kasar Sin za ta ci gaba da yayata bukatar ganin an raba riga kafin a duniya dai-dai wa daida.

Zhao wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, ya ce kasar Sin, tana ba da muhimmanci kan tsaro da inganci riga kafin a gaban komai, tana kuma tabbatar da cewa, kamfanonin samar da riga kafin, sun bi matakai da ka’idoji na kimiyya wajen gudanar da cikakken bincike wajen samar da riga kafin.

Ya kara da cewa, kasar Sin ta kudiri aniyar ganin riga kafin COVID-19, ya kasance hajar daukacin al’ummar duniya. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ko dai ta samar ko kuma tana shirin samarwa kasashe 53 tallafin riga kafin, a hannu guda kuma, kamfanoninta sun fitar ko suna fitar da riga kafin zuwa kasashe 27(Ibrahim)