logo

HAUSA

An yi taron yabawa wadanda suke ba da babbar gudunmawa wajen kawar da talauci a kasar Sin

2021-02-25 11:18:31 CRI

An yi taron yabawa wadanda suke ba da babbar gudunmawa wajen kawar da talauci a kasar Sin_fororder_8d5494eef01f3a29ca7dc206eaf6a6395e607c98

An yi taron yabawa wadanda suke ba da babbar gudunmawa wajen kawar da talauci a kasar Sin a yau Alhamis a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tare da ba da jawabi.

Tun lokacin da aka kira babban taron wakilan ‘yan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18, Sin ta aiwatar da shirin yaki da talauci mafi girma da karfi a kasar. Shekaru 8 da suka gabata, an fitar da gundumomi 832, da kauyuka dubu 128, da ma manoma fiye da miliyan 100 da suka sha fama da talauci daga kangin talaucin, matakin da ya zama abun ban mamaki ga duniya wajen tallafawa matalauta.

Haka zalika kasar Sin ta cimma nasarar daidaita matsalar kangin talauci, wasu shekaru 10 kafin wa’adin cimma muradun kawar da talauci da MDD ta tabbatar, bisa ajandar neman samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030. (Amina Xu)