logo

HAUSA

Dan kwallon kasar Sin Wu Lei na farin cikin taka leda a Espanyol

2021-02-25 21:20:23 CRI

Dan kwallon kasar Sin Wu Lei na farin cikin taka leda a Espanyol_fororder_0225-2

Dan kwallon kasar Sin Wu Lei na farin cikin taka leda a Espanyol_fororder_0225-1

Yayin da kungiyar kwallon kafa ta kasar Sifaniya, wato Espanyol ke kokarin sake komawa gasar kwararru aji na daya ta kasar wato La liga, dan wasan kasar Sin Wu Lei dake taka leda a kungiyar, na fatan kara samun kwarewa, da jin yadda kwallon kafa take a Sifaniya.

Wu ya fara bugawa Espanyol kwallo ne shekaru 2 da suka gabata, ya kuma sha dadi, da wuyar kwallo a wannan kungiya dake da mazauni a birnin Barcelona, ciki har da lokacin da kungiyar ta kai ga samun gurbin buga wasan kungiyoyin nahiyar Turai a kakar sa ta farko a kungiyar, kafin daga bisani ta fado cikin jerin kulaflikan da suke buga wasa a mataki na 2, wato rukunin “Liga SmartBank” a kakar da ta gabata.

A wannan gaba da Espanyol ke kan ganiyar neman damar sake komawa buga gasar La Liga, cikin jerin kungiyoyin dake buga Liga SmartBank, dan wasan ya yiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua karin haske, game da rawar da ya taka a kungiyar, da kuma burin sa game da kwallon kafa.

Wu ya fara da bayyana burin sa a Sifaniya, yana mai cewa "na zo Sifaniya ne domin na koyi darasi da kwarewa. Baya ga kwallo a wannan kasa, ina kuma son fahimtar al’adun Sifaniya. A shekaru 2 da suka gabata, na koyi abubuwa, kana na gane wasu batutuwa masu nasaba da tsarin taka leda a La Liga, da La Liga Smartbank,".

Ya kara da cewa "A kakar bana, na lura da tsarin wasanni a rukuni na biyu na ajin kwararru, inda kowa ke kokarin farfadowa, hakan ya kuma haskaka min dukkanin yanayin kwallon kafa a sassa 2, na ajin kungiyoyin dake buga kwallo a Sifaniya. Wu ya ce wannan dalili ya sa bana jin kewar gasar La Liga, yayin da muke buga kwallo a rukuni na 2 na ajin kwararrun Sifaniya.

Wu ya samu karbuwa da shahara sosai, jim kadan bayan zuwan sa Sifaniya a watan Fabarairun shekarar 2019, da kuma lokacin da ya ci kwallon sa ta farko ga Espanyol, wadda ta kasance ta farko da wani Basine ya taba ciwa kungiyar, a lokacin ne ma magoya bayan kungiyar suka fara yi masa lakabi da "Fatan dukkanin kasar Sin".

To sai dai kuma a karshen wannan kaka, Espanyol ta fada kasan tebur, wanda ya haifar mata da komawa aji na 2, na masu buga kwallon kafar Sifaniya. Don da haka dan wasan na Sin, na da burin taimakawa kungiyar sake komawa buga gasar La Liga, ya kuma ce yana da kwarin gwiwa sosai na cimma wannan buri.

Ya zuwa yanzu, dan wasan mai shekaru 29 da haihuwa ya bugawa kungiyar wasanni 19, inda ya yi zirga zirga ta mintuna 627, kuma duk da matsakaicin hakan bai wuce mintuna 33 a wasannin da ya buga ba, wato kasa da mintuna 52 da ake son dan wasa ya yi a kaka guda, ya ce bai damu ba, game da tunkarar karin takara daga sauran ‘yan gaban kungiyar, irin su Raul de Tomas, duba da cewa tun zuwan sa kungiyar yake fama da irin wannan takara, don haka ya saba da hakan.

Wu ya ciwa kungiyar sa kwallaye 2 a gasar “Copa del Rey”, kuma game da hakan ya ce, duk da kasancewar ya gamsu da tsarin kungiyar na taka leda, amma hakan bai hana shi ci gaba da nazarin tasirin sa a kungiyar ba.

Ya ce "Batun dai duk a kai na ne," musamman lokacin da ya tabo batun farkon barkewar annobar COVID-19 a watan Maris na shekarar 2020, lokacin da ya bayyana a matsayin mai matukar wahala.

Dan wasan da dukkanin iyalan sa sun harbu da cutar, sun kuma killace kan su, tare da katse alaka da abokai da abokan wasan sa. Game da hakan, Wu ya ce "A hakikanin gaskiya, na rika jin tamkar na koma gida Sin. Amma kuma a wannan lokacin, da yake ina tare da iyalai na, da magoya baya masu nuna min kauna, ni da iyalai na mun kai ga farfadowa.

Ya kara da cewa, dokokin da ake aiwatarwa a yanzu, wadanda suka tanaji buga kwallo ba ‘yan kallo, don dakile yaduwar cutar, su ma sun rage kaskashin sa.

Ya ce "Na dade ina fadar cewa ‘yan kallo ne kashin bayan karfin gwiwar ‘yan wasa. Yanzu da ba bu su, yanayin wasa ya zama mai matukar wahala, sai dai duk da haka ina fatan wannan cuta za ta wuce, ta yadda ‘yan kallo za su sake dawowa kallon mu, mu ci gaba da mishadi tare da su."

Wu ya ce duk da koma bayan da kungiyar sa ta fuskanta a bara, shawar sa ta ci gaba da zama a Sifaniya a kakar bara ta yi ma’ana.

Ya ce "A shekaru na yanzu, sabawa da rayuwar Turai, da iya ci gaba da zama a nan, sun sa ina jin bai dace na yi “da na sani ba”. Akwai kuma batun iyali. Iyali na suna farin ciki, don haka ina ga na yanke shawara mai kyau.