logo

HAUSA

Jami’in MDD ya ayyana bangarori 4 don magance sauyin yanayi dake barazana ga zaman lafiya da tsaro

2021-02-24 10:46:38 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana wasu bangarori hudu da ya kamata kasa da kasa su baiwa fifiko, domin shawo kan manyan hadarorin sauyin yanayi, dake barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, wanda ya kunshi mayar da hankali wajen daukar matakan kandagarki mai karfi, domin cimma burin aiwatar da matakan magance matsalolin sauyin yanayi.

Jami’in MDD ya bayyanawa babban taron mahawara na kwamitin sulhun MDD, game da yaki da sauyin yanayi da tsaro, wanda aka gudanar ta kafar bidiyo cewa, da farko, ya kamata a mayar da hankali wajen daukar matakai masu karfi na kandagarki, da aiwatar da matakan yaki da sauyin yanayi na zahiri.

Batu na biyu da ya dace a baiwa fifiko, babban jami’in MDDr ya ce, akwai bukatar gaggauta aiwatar da matakan da za su baiwa kasashen duniya kariya, musamman ga al’ummomin yankunan dake fama da karuwar matsalolin tasirin sauyin yanayi.

Na uku, Guterres ya ce, ya kamata a rungumi tsarin tabbatar da tsaro, wanda ya baiwa rayuwar mutane fifiko a sama da komai.

Da yake bayani game da bangaren da za a baiwa fifiko na karshe, Guterres ya ce, kamata yayi a zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashe sama da tsarin MDD kadai.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson, shi ne ya jagoranci tattaunawar, wanda ya kasance a karon farko da firaministan Birtaniya ya jagoranci taron kwamitin sulhun MDD tun wanda John Major, ya jagoranta a watan Janairun 1992.(Ahmad)

Ahmad