logo

HAUSA

A kalla mutane 67 ne suka mutu yayin tarzoma a wasu gidajen yarin Ecuador

2021-02-24 10:40:37 CRI

Daraktan sashen lura da bukatun baligai da suka rasa ‘yancin su a gwamnatin kasar Ecuador Edmundo Moncayo, ya ce a kalla mutane 67 ne suka rasu, lokacin da kungiyoyin ‘yan daba da ba sa ga maciji da juna, suka yi fito na fito a wasu gidan yari 3.

Mr. moncayo ya shaidawa manema labarai cewa, an samu asarar rayukan ne a gidajen yarin lardin Guayas dake kudu maso yamma, da na Cotopaxi dake tsakiya, da kuma na Azuay dake kudancin kasar, wuraren da su ke dauke da kaso kusan 70 bisa dari na daukacin gidajen yarin kasar.

Rahotanni daga rundunar ‘yan sandan kasar sun nuna cewa, an samu barkewar tashin hankali a gidajen yarin ne da safiyar jiya Talata, sakamakon sabani tsakanin sassan ‘yan dabar dake tsare.

Tuni dai gwamnatin kasar ta amince da tura ‘yan sanda masu damara gidajen yarin, domin dawo da doka da oda.  (Saminu)

Saminu