logo

HAUSA

Gudummawar WHO ta rigakafin Ebola 11,500 ta isa kasar Guinea

2021-02-23 10:48:18 CRI

A jiya Litinin ne ma’aikatar lafiya ta kasar Guinea, ta karbi gudummawar rigakafin cutar Ebola 11,500 daga hukumar lafiya ta duniya WHO.

Wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar ta fitar, ta ce za a yiwa al’ummun lardin N'Zerekore dake kudu maso gabashin kasar rigakafin, domin dakile yaduwar cutar zuwa sauran sassan kasar.

Alkaluman hukuma sun nuna cewa, ya zuwa yanzu, an samu mutane 17 dauke da cutar a Guinea, ciki har da 5 da suka rasu, akwai kuma wadanda suka yi cudanya ta kusa da masu dauke da cutar su 380, kuma 371 daga cikinsu na samun kulawar jami’an lafiya domin tantance matsayinsu.

A ranar 14 ga watan nan na Faburairu ne ma’aikatar lafiyar kasar Guinea, ta tabbatar da sake bullar cutar Ebola a lardin N'zerekore, inda aka tabbatar da harbuwar mutane 7, ciki har da 3 da suka rasu.   (Saminu)