logo

HAUSA

Baki ‘yan kasashen waje sun yabawa kasar Sin saboda babbar nasarar da ta samu wajen kawar da talauci

2021-02-23 12:39:01 CRI

Tun da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekara ta 1978, kawo yanzu, miliyoyin Sinawa sun fita daga zaman talauci, al’amarin da ya ba da gudummawar kaso 70 bisa dari na daukacin ayyukan yaki da talauci a duniya.

Akwai baki ‘yan kasahen waje da yawa wadanda ke zaune a kasar Sin, wadanda kuma su ne masu gani da ido, game da babbar nasarar da kasar ta samu a fannin yaki da talauci. A nasu ra’ayi, kasar Sin ta samarwa duk duniya dabarunta na yaki da talauci.

Sautin da kuke ji yanzu, na wani bidiyo ne wanda wani dan kasar Isra’ila mazaunin kasar Sin mai suna Raz Galor, gami da kungiyarsa suka dauka, dangane da yadda ake yaki da talauci a yankunan karkarar kasar Sin. Raz Galor, wanda ya yi shekaru 13 yana zaune a kasar, ya kafa wata kafar yada labarai mai zaman kanta, wadda ke daukar bidiyo masu nasaba da halin da ake ciki a kasar Sin, domin tallata kasar ga duk duniya baki daya.

Raz Galor ya ce:

“A shekarun nan, manufofin da gwamnatin kasar Sin ta tsara na yaki da talauci, sun lalibo mata wata hanyar da ta dace, ta kara cimma nasarori fiye da na lokacin baya. Abun da ya sa na kara fahimtar mene ne ainihin aikin kawar da talauci. Wato zai iya samar wa mutanen dake fama da talauci wani tsarin zabi na zamani, ta yadda za su iya kara samun kudin shiga.”

Raz Galor yana himmatuwa wajen tallata ayyukan yaki da talauci da kasar Sin take yi ga kasashen ketare, ta hanyar daukar gajeren bidiyo, inda a cewarsa, bidiyon na samun karbuwa sosai, da jawo hankali a dandalin sada zumunta na ketare.

“Bidiyon da muka dauka sun samu amincewa da karbuwa sosai a kasar Indiya da nahiyar Afirka, kuma masu kallo sun jinjinawa hakan sosai, har suna cewa akwai bukatar irin wannan kokari a kasashen su.”

Tamkar abun da Raz Galor ke yi, wani dan kasar Japan mai suna Hiroto Kawasaki, shi ma yana ganewa idanunsa yadda kasar Sin take kokarin yaki da talauci. Hiroto Kawasaki, mai shekaru 74 a duniya, ya yi shekaru kusan 7 yana aiki a wani filin noma dake gundumar Yuanyang ta lardin Henan na kasar Sin.

Da misalin karfe 6 na safiyar kowace rana, Hiroto Kawasaki ya kan tashi daga barci. Bayan karya kumallo, ya kan je duba yadda ake sarrafa takin zamani, daga baya ya kan je aikin kawar da ciyayi, da duba yadda amfanin gona suke tsirowa a gonaki.

Filin noman da Hiroto Kawasaki yake ma aiki, mai suna Xiaoliugu, yana gundumar Yuanyang dake lardin Henan, wadda da ma gunduma ce mai fama da kangin talauci. A ‘yan shekarun nan, Hiroto Kawasaki ya shaida matukar kokarin da ake yi na kawar da talauci a wurin, inda ya ce:

“A halin yanzu, rayuwar al’ummar kasar Sin na kara kyautata. An kara kafa manyan rumfuna da filayen kiwon kaji, da sauran dabbobi a yankunan karkara. Kila kasar Sin ita kadai ce wadda ke dora muhimmanci sosai kan aikin kawar da talauci, da zuba makudan kudade a wannan fanni.”

Shi ma a nasa bangaren, wani dalibi dan asalin kasar Tajikistan wanda ke karatu a yanzu haka a Beijing, Kamolov Mehroj, ya samu fahimta sosai game da sauye-sauye da ci gaban da kasar Sin ta samu sakamakon kokarin yaki da talauci, inda ya ce:

“Kasar Sin na nuna kwazo wajen taimakawa mutanen dake fama da talauci, da samar musu da zaman jin dadi, da warware musu matsalolin rayuwar da suke fuskanta. A wasu sassa masu nisan gaske, gwamnatin kasar ta kafa masana’antu, da samar da guraban ayyukan yi ga mazauna wuraren, don taimaka musu yaki da talauci.”

Joshua Dominick, ba’amurke ne wanda ya yi shekaru 20 yana aiki a kasar Sin, ya ce, aikin kawar da talauci da kasar Sin take gudanarwa, ya zama tamkar abun koyi ga aikin kawar da talauci a duniya:

“Kasar Sin tana bayar da dabarunta ga duniya. Kasashen dake da makusancin halin bunkasuwa da ita, suna iya koyi daga wajen ta.  Kasashe masu hannu da shuni kuwa, su ma za su iya yin koyi da wasu abubuwa daga kasar ta Sin.”(Murtala Zhang)