logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci a samar da mafita ga rikicin siyasar Somalia

2021-02-23 11:27:01 CRI

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD, Dai Bing, ya yi kira ga dukkan bangarori a Somalia, su lalubo mafita mafi dacewa ga rikicin siyasar kasar.

Dai Bing, ya shaidawa taron Kwamitin Sulhu na MDD da ya gudana ta kafar bidiyo cewa, Sin ta damu da rikicin da ya auku kwanan nan a Mogadishu. Don haka take kira ga bangarorin kasar su kai zuciya nesa, su tattauna tare da samar da mafitar da ta dace nan bada dadewa ba.

Ya kuma bayyana fatan za a gudanar da zabe a kasar nan bada jimawa ba, domin dawo da zaman lafiya, da samar da kyakkyawan muhallin mayar da hankali kan kokarin gina kasa.

Game da batun tsaro a kasar kuwa, Dai Bing ya ce Sin na goyon bayan bangarorin su karfafa tuntuba dangane da sabunta aikin shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika a kasar, domin samar da mafitar da za ta karbu ga kowa.

Ya kuma yi alkawarin Sin za ta samar da taimakon riga kafin COVID-19 ga kasar idan ta bayyana bukata. (Fa’iza Mustapha)

Faeza