logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya yi kira da adalci wajen rabon alluran riga kafin COVID-19

2021-02-23 11:21:51 CRI

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya jaddada bukatar tabbatar da riga kafin COVID-19 ya zama hajar da duk duniya za ta samu cikin rahusa.

Antonio Guterres, ya bayyana yayin bude taron majalisar kare hakkin dan Adam na majalisar karo na 46 cewa, adalci wajen rabon riga kafin shi zai tabbatar da kare hakkin bil adama, yayin da ba wata kasa fifiko ke zaman kishiyar hakan.

Ya ce annobar ta kara haifar da bambanci da rauni da rashin daidaito da ke akwai, yana mai cewa ta yi mummunan tasiri kan mata, da marasa rinjaye, da mutane masu bukata ta musammam, da tsoffi, da ‘yan cirani, da masu hijira, da ‘yan asalin wurare.

Ya kara da cewa, an samu koma bayan shekaru, dangane da nasarorin da aka samu ta fuskar daidaiton jinsi, inda tsananin talauci ya karu, a karon farko cikin gomman shekaru.

Sakatare Janar din ya nanata burin kare hakkin bil adama na majalisar, yana mai cewa, abun da ya kamata a mayar da hankali kai shi ne, wariyar launin fata, da kyama, da kin jinin baki, da ma wariyar jinsi. (Fa’iza Mustapha)

Faeza