logo

HAUSA

Jami’ar Johns Hopkins: Yawan mamata a Amurka sakamakon COVID-19 ya zarce dubu 500

2021-02-23 11:30:34 CRI

Jiya Litinin, jami’ar Johns Hopkins ta ba da alkaluma kan cutar COVID-19 cewa, ya zuwa karfe 4 da mintoci 24 na yammacin jiya agogon gabashin Amurka, yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar ya kai 500,071, kana yawan mutanen da suka harbu da cutar ya kai 28,174,133.

Yawan mamata sakamakon cutar ya rika karuwa, kididdigar da aka bayar na nuna cewa, wannan adadi ya karu zuwa dubu 200 daga dubu 100 a cikin watanni kasa da 4, kuma karuwarsa zuwa dubu 300 bai wuce watanni 3 ba, yayin da ya karu zuwa dubu 400 da dubu 500 a cikin wata daya da wani abu.

Tawagar nazarin kwayar cutar COVID-19 ta jami’ar ta tattara wadannan alkaluma ne daga yankuna daban-daban cikin lokaci. (Amina Xu)