logo

HAUSA

Xi Jinping ya zanta da takwaransa na Masar

2021-02-23 11:51:39 CRI

Jiya Litinin da dare, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Masar, Abdel Fattah al Sisi ta wayar tarho.

Xi Jinping ya ce, kasar Masar ita ce kasa ta farko, wadda ta kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin cikin dukkanin kasashen Larabawa da kasashen Afirka, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta kasance abin koyi game da yadda ake aiwatar da hadin gwiwa da cimma moriyar juna a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa da ma kasashen Afirka. Kasar Sin tana fatan ci gaba da karfafa fahimtar siyasa a tsakanin bangarorin biyu, domin goyon baya ga juna, da kuma karfafa hadin gwiwar kasashen biyu cikin harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda za a kiyaye tsarin hadin gwiwar dake tsakanin sassa daban daban, da yanayin adalci na duniya.

Shugaba Xi ya kara da cewa, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin da kasar Masar sun samar wa juna kayayyakin yaki da cutar cikin gaggawa, lamarin da ya nuna zurfin zumunci dake tsakanin bangarorin biyu. A nan gaba kuma, kasar Sin tana fatan hada gwiwa da kasar Masar kan harkoki masu nasaba da allurar rigakafin cutar COVID-19, da goyon bayan kasa da kasa wajen yaki da annobar cikin hadin gwiwa, ta yadda za a inganta dunkulewar dukkanin bil Adama a bangaren kiwon lafiya.

A nasa bangaren kuma, shugaba Abdel Fattah al Sisi ya taya Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin murnar cika shekaru 100 da kafuwa. Ya ce, bana shekara ce ta cika shekaru 65 da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Masar. Kasarsa tana goyon bayan kasar Sin kan harkokin dake da nasaba da yankin Hong Kong, jihar Xinjiang da yankin Taiwan na kasar, tana kuma tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan kasar Sin a fannonin kare ’yancin kai da tsaro da kuma cikkaken zaman kasa. Kana, kasar Masar na adawa da dukkanin matakan da wasu kasashe suka dauka domin tsoma baki cikin harkokin kasar Sin, bisa hujjar hakkin dan Adam.

Bugu da kari, ya ce, yana maraba da zuwan kamfanonin kasar Sin kasarsa domin zuba jari ko kuma hadin gwiwa. Ya ce Masar na fatan hada kai da kasar Sin domin daga dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu. A karshe dai, ya godewa kasar Sin bisa goyon bayan da take baiwa kasashen Afirka da ma dukkanin kasashe masu tasowa a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, yana fatan karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin kan harkokin dake shafar allurar rigakafin cutar COVID-19. (Maryam)