logo

HAUSA

Wakilin Sin ya musanta kalaman rashin gaskiya da jami’in diflomasiyyar Burtaniya ya yi cikin taron MDD

2021-02-23 15:46:22 CRI

Jiya Litinin, kakakin zaunanniyar tawagar wakilan kasar Sin dake MDD dake birnin Geneva, ya ba da jawabi a babban taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD, inda ya musanta kalaman rashin gaskiya da jami’in diflomasiyyar kasar Burtaniya ya yi, dangane da harkokin dake shafar jihar Xinjiang,da jihar Tibet, da yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Jami’in na Sin ya ce, kasarsa ta bukaci kasar Burtaniya da sauransu, su mai da hankali kan matsalar hakkin dan Adam cikin kasashensu, a maimakon siyasantar da batun hakkin dan Adam, da kuma bata suna na sauran kasashen duniya bisa labarai na jabu. Kuma ya kamata su ba da gudummawa ga bunkasuwar harkokin kare hakkin dan Adam tsakanin kasa da kasa, a maimakon yin amfani da batun hakkin dan Adam wajen cimma mugun burinsu a fannnin siyasa. (Maryam)