logo

HAUSA

Abubakar Muhammed Sadiq: Ci gaban kasar Sin ya burge ni

2021-02-23 14:09:20 CRI

Abubakar Muhammed Sadiq: Ci gaban kasar Sin ya burge ni_fororder_微信图片_20210223133139

Abubakar Muhammed Sadiq, wani dan arewacin Najeriya ne wanda a yanzu haka yake karatu a jami’ar Tianjin dake arewacin kasar Sin. A zantawarsa da Murtala Zhang, Abubakar Sadiq ya bayyana dalilin da ya sa ya kuduri aniyar karo ilimi a kasar Sin, da Hausawa ke kira bangon duniya. Sa’annan ya kwatanta yanayin karatu tsakanin gida Najeriya da kasar Sin, gami da yadda yake mu’amala da al’ummar kasar Sin.

Abubakar Muhammed Sadiq: Ci gaban kasar Sin ya burge ni_fororder_微信图片_20210223133146

Abubakar Sadiq, wanda ya shafe shekaru kusan biyar a kasar Sin, ya bayyana ci gaban kasar a ganinsa, musamman fasahar sadarwar zamani ta 5G, da kuma yadda gwamnatin kasar take kokarin ganin bayan annobar COVID-19. Har wa yau, ya bayyana ra’ayinsa kan wasu al’adun gargajiya na kasar ta Sin.

A karshe, Abubakar Sadiq ya bayyana fatansa ga matasan Najeriya da ma daliban kasar da suke karatu a yanzu haka a China. (Murtala Zhang)